Yadda Ake Gyaran Jiki Da Gyaran Nono a Saukake

Gyaran Jiki

Na tabbata akwai tarin ‘yan ‘uwa mata da ke matukar bukatar tsumummuka da hadidddika na gyaran jiki da gyaran nono kamar ba gobe, kuma har yanzu neman sadidan suke.

Abin kam na da matukar cin rai da zuciya ace jikinki na wari, ko kuma ace mamanki (nono) ya zube ya daina tsaiwa ko da kuwa ba kamar da lokacin da kike budurwa ba.

Ba yaudarar kai, na sani, kin sani, mun sani, babu yadda nonon babbar mace ko mai aure wacce ba shayarwa take ba zai tsaya a tsaye kyam yana kallon gaba muddin ba budurwa ce ba.

Kai wani abin ban mamaki shi ne; yadda za ka ga budurwa da zubabben nono, sai ka rasa ta yaya ta yi sakaci suka zube.

Wacce ke da wannan matsalar na yi imani da Allah za ta ji ba dadi, kuma na tausaya mata.

{tocify} $title={Table of Contents}

Wacce kuwa ke da matsalar warin jiki, ko warin kashi ko kuma ita din dai kazama ce, to, na san ita ma za ta ji babu dadi, sa’annan dole ne a tausaya mata.

Bisa wadannan tarikan dalilai da ma wadanda ban zayyano ba, mai gudanarwa (admin) na wannan gida mai albarka ya ga ya dace ya yi binciken kwakwaf a yanar gizo da wurin masu bada tsumummuka domin kawo muku mafita wacce ba za ku yi nadamarta ba.

Da fatan ‘ya ku iyaye mata za ku yi wa Allah godiya sannan kuma ku salahewa yaranku su je su yi karatun na’ura mai kwakwalwa domin bada gudunmawa ga al’umma.

Gyaran Jiki

Jiki kowanne iri ne (walau na mace ko namiji) na da matukar bukatar gyara da tsafta, hakan ya sanya tsafta ta zamo cikin addini. 

A wurin su kuwa ‘yan uwa mata, gyaran jiki a wanke shi, a sulle shi, a tsaftace shi, a fesa turare, ana tafiyar yanga wajibi ne.

Hakan ya sa za mu kawo wasu tarin hadi-hadi na gyaran jiki akalla nau’ika biyar zuwa sama, daga nan sai mu kawo muku hadi na gyaran nono.

Hadin Gyaran Jiki (Madara da Lemon Tsami)

Madallah, yanzu zan kawo wani irin hadi na gyaran jiki wanda ake yinsa da madara da kuma lemon tsami.

Bugu da kari, in dai aka juri yinsa akai-akai, za a ga fatar jiki tana kara haske matuka gaya.

Also Read: Koyi Yadda Ake Yin Lallen Gam Da Lallen Du-kafa Cikin Sauki

Kai ba ma iya haske yake kara wa ba, har ma da laushi fata. Kin ga kuwa cinyewa ce a gareki ‘yar‘uwa jikinki ya yi laushi luwai ba tare da kin kara kiba ba.

Yadda Ake Hada Shi

Da fari da ki samu madararki ta gari ki jikata sannan sai ki matse wannan lemon tsamin naki a ciki. Bayan kin gama matsewa sai kuma ki gauraya.

Kina kammala gaurayawa sai ki shafe fuskarki, hannunki kai har ma da dukkanin jikinki.

Ya danganta da bukatarki; in iya hannu da fuska kike son su yi haske hadi da laushi to sai ki shafesu, in ko ko ina kike son ganin ya yi luwai-luwai da haske sai ki yi azama.

Bayan kin gama shafewa, sai ki barshi na akalla tsawon mintuna biyar haka, daga nan za ki iya wankewa da ruwan dumi .

Da yardar Allah in dai kina yin irin wannan hadin akai-akai za ki ga yadda jikinki zai sauya.

Hadin Gyaran Jiki (Ayaba da Kindirmo da Zuma)

Na tabbata wasu za su yi mamaki ta yaya za a hada hadin gyaran jiki da ayaba da kindirmo?

Amma bin matukar sauki gareshi.

Ki samu ayaba guda biyu a bare sai a samo kindirmo luddai daya, da zuma a hada su wuri guda a saka a mamarkadi a markada su yadda ya kamata.

Daga nan sai a shafe duk inda ake da bukatar ya yi kyau a jiki (walau fuska da hannu ko kuma gaba daya jiki).

Aradun Allah wannan hadin ya fi wanda muka fara kawowa tasiri a jikin mace, abin kam sai wanda ya gwada. Kuma ana da bukatar a rinka rinsa akai-akai, ko da irin 2 to 3 times per week din nan ne.

Duk wadannan nau’ikan hadin gyaran jikin guda biyu da na zayyano a sama babu wanda ba ya da tasiri a jikin dan Adam.

Kuma suna da matukar yawa, amma wadannan sun fi yin shura.

Za ku jini da wasu da zarar bincikena ya zo kansu, kuma an gwada an tabbatar suna yin aiki.

Yanzu kuma za mu gangara kan hadin gyaran nono, wanda ina da tabbacin da dama daga cikin ‘yan‘uwa mata suna da muradin samun irin wadannan hadiddika da zan kawo.

Gyaran Nono

Nono shi ne adon kowacce mace in ka dauke adon fuskarta da kirarta. Eh mana, mafi akasarin maza in suka hadu da mace kafin su fara kallon fuskarta sai sun sauke idanuwansu akan kirjinta sannan daga baya su dago idanunsu zuwa fuskarta.

Kada ki yi mamaki don kin ji na fadi haka domin ni ma namiji ne, na san ya lamarin yake.

To, sai kuma aka samu akasi, kirjin mace ya zube ya yi rabebe yaya kenana?

Wallahi ta baci, bacin ma ba dan karami ba, hakan ya sanya mata da yawa yin farautar hadi-hadi da ke taimakawa wurin dawo da tsaiwar nono bayan ya zube.

Kuma ni ban ga laifinsu ba, domin hakan ya zama wajibi saboda a cikin maza ba kowa ke son mace marar nono ba, sai dai in ba yadda ya iya.

Hadin Gyara Nono (Zubewarsa)

In har kina daya daga cikin wadanda nononsu ya zube, to gaskiya wannan hadin naki ne.

Na san abin akwai ciwo, amma babu yadda aka iya. Bisa wagga dalili ki samo;

  1. Alkama
  2. Gyada
  3. Ridi
  4. Danyar shinkafa
  5. Busasshen karas (shi ne ma nake tunanin zai yi wuya in dai ba danye za ki saya ki shanyashi ya bushe ba)
  6. Habbatussauda
  7. Hulba

Bayan kin samo duk wadannan abubuwan guda bakwai (7) da na lissafo, sai ki hada su wuri guda ki daka su, daga nan sai kina amfani da shi lokaci zuwa lokaci, amma fa akai-akai.

Hadin Gyaran Nono (Mikakke)

Na tabbata za ki yi matukar farin ciki in dai mamanki wanda ya zube ya kankance ki ka ga ya fara cikowa yana mikewa.

Domin yin wannan farin cikin sai ki samo;

  1. Garin gero
  2. Zuma
  3. Madara
  4. Da albasa ‘yar madaidaiciya

Bayan kin samo, sai kuma ki biyo wadannan matakan da zan kawo domin ki hada wannan hadin.

Da fari dai albasarki za ki fara samu madaidaiciya, ki saka wuka ki yayyakata, ki hura wuta, ki zuba ruwa a cikin tukunya in ya tafasa sai ki zuba albasarki.

Ruwan nan yana komawa baki (wato lokacin ta dafu) sai ki juye shi, ki samo garin gero luddai guda, da madararki ‘yar gwangwani (kamar peak guda daya ta ruwa) da zumarki mai kyau.

Kina samo su, ki juye su a cikin ruwan, amma fa ki debi wanda za ki iya shanyewa a ranar.

Bayan kin hada su da ruwan albasar kin gauraya, sai ki bari ya yi sanyi sannan ki sha.

In dai kika juri yin hakan ko da a sati sau uku ne, da yardar Allah za ki ga canji.

Kammalawa

A zahirin gaskiya ban so na tsaya a iya nan wurin ba, amma kuma saboda ina son kada rubutun ya yi matukar tsayi dole na tsaya. Mun tattauna akan gyara jiki da gyaran nono, kuma nan bada jimawa ba, admin din gidan nan zai saki littafin gyaran jiki wanda Insha Allahu za mu wallafa labarin sakinsa a shafin nan.

Ku yi sharhi.

Previous News Next News