Wasu Marasa Imani sun Azabar Tare da Kashe Wani Mutum Akan Satar Kankanar N2,000 a Bauchi

Mai Laifi
Masu Laifin Guda Hudu

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce ta cika hannu da wasu mutane hudu da ake zargi da azabtar da wani da ake zargin barawon kankana ne wanda hakan ya yi sanadiyyar shekawarsa lahira.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jihar.

Ya ce an kama marigayin ne bayan da ya saci kankana guda bakwai da kudinsu ya kai Naira 2,000 a wata gonar rani da ke kauyen Dallaji da ke unguwar Tudin Wada a karamar hukumar Warji a jihar Bauchi.

Sufeton ‘yan sanda Wakili ya ce: “A ranar 29 ga Maris, 2023 da misalin karfe 10:00 na safe, wani Ado Sanya mai shekaru 40, mazaunin kauyen Dallaji, Tudun Wada, karamar hukumar Warji, ya kawo rahoto a hedikwatar ‘yan sanda ta Warji inda ya bayyana musu cewa da misalin karfe 1:20 na dare jiya, an kama wani mai suna Ibrahim Hashimu a gonar wani Mohammed Garba kan laifin satar wasu kwallayen kankana.

“Masu gonar sun kuma daure hannun barawon (Ibrahim Hashimu) biyu ta baya da igiya inda suka hau kansa da duka da sanduna sai da suka yi masa lilis.

“Wadanda suka yi wannan aika-aikar sun hadar da Mohammad Daluta (dan shekaru 24),da Ibrahim Mahmud (dan shekaru 22), da Bashir Mahmud ( dan shekaru 18) sai Abdullahi Mahmud (dan shekaru 22).

“Da samun rahoton, sai aka yi gaggawar kai tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda aka dauki wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Warji domin kula da lafiyarsa, inda suka kai asibitin Cottage da ke karamar hukumar Gwaram a Jihar Jigawa, inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa. .

"Bincike da aka fara cikin tsanaki da bincike na farko ya nuna cewa wanda aka kashe "Ibrahim Hashimu" ya kutsa kai cikin gonar noman rani inda ya sace 'ya'yan kankana guda bakwai wanda kudinsu ya kai N2,000.

"Saboda haka, an samu nasarar kama dukkan wadanda ake zargi guda hudu kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano duk wasu kura-kurai da suka dabaibaye lamarin."

A cewarsa, Kwamishinan ‘yan sandan, Aminu Alhassan, yayin da yake mayar da martani kan lamarin, ya fusata da matakin da wadanda ake zargin suka dauka, inda a maimakon su kai rahoto ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu, sai suka dauki doka a hannunsu.

“Duk da haka ya ba da umarnin a mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na Bauchi, domin gudanar da bincike na gaskiya, ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a yi adalci a kan haka.”

Hakazalika, PPRO ya ce a ranar 24 ga Maris, 2023 da misalin karfe 10:09 na dare wasu da ba a san ko su wanene ba, suka kutsa cikin gidan wani mai suna Abdu Muhammadu (30) da ke kauyen Dasare, unguwar Tarbuwa a karamar hukumar Zaki ta jihar Bauchi, suka dirka masa kibiya a kirjinshi.

Ya ce a dalilin haka ya samu munanan raunuka; Ya kara da cewa, bayan samun bayanan sirrin faruwar lamarin a ranar 26 ga Maris, 2023 da misalin karfe 12:30 na safe, jami’an ‘yan sanda da ke hedikwatar Zaki reshen Zaki karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda, sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka dauki wanda abin ya faru zuwa cibiyar lafiya ta tarayya, Azare, domin a yi musu magani cikin gaggawa, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Previous News Next News