Sauke Sabuwar Wakar Rarara Mai Taken, “Baba Ya Sauka Da Kwari”

Baba Ya Sauka Da Kwari
Rarara da Tinubu

Magana ta gaskiya, tun bayan da Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya saki wakar, “Buhari Ya Dawo” ban yi tunanin zai dawo da wata irin wakar mai kamanceceniya da wannan ba ya kara yi wa wani dattijon.

A nan dattijon da nake nufi shi ne; sabon angon Najeriya, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

{tocify} $title={Table of Contents}

Hmm, duniya mai yayi.

Kusan kowa ya san Rarara mawakin Buhari ne na gani kasheni, amma yanzu kam ya yi juyi, ya koma dan gidan Tinubu.

Baba Ya Sauka Da Kwari

Ina daukacin masoya wakokin Dauda Kahutu Rarara? To sai gareku domin ya saki sabuwar wakarsa mai taken, “Baba Ya Sauka Da Kwari” wacce ya yi wa Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.

Sannan a cikin wakar ya yi wadansu kalamai wadanda suka matukar yamutsa hazo a kafafen sada zumunta musamman tiktok, facebook da instagram

Idan ba ku manta ba, a baya, tsulawa (yaran Kwankwasiyya) sun yi masa cin mutunci na Allah ya tsine uwar mai karya sakamakon shaguben da yake yi wa ubangidansu (Wanda su a wurinsa daukar da suka yi masa ubansu ne).

You Might Also Like: Sauke Sabuwar Wakar Rarara Mai Taken “Tangal Tangal” Da Kuma Karanta Dalilin Sakinta

Hakan ya sanya suka rinka zaginsa da cin zarafinsa, abin ba a iya nan ya tsaya ba har uwarsa sai da suka zaga.

Me Ya Faru?

Biyo bayan ruwan kwandunan rashin darajar da yaran tsula suka sauke wa Rarara, sai ya ‘dan shiga taitayinsa musamman a cikin wannan sabuwar wakar tasa ta baba yau sauka da kwari.

Ya Kai Karar Yaran Tsula

Babu wanda in ya ji wuta, ba zai dan sarara ba sai dai in wutar ba ta kai wuta ba.

A cikin sabuwar wakar nan tasa kam ya ‘dan sarara domin bai yar musu da magana ba.

Amma kuma muna jiran sabuwar wakarsa ta gaba domin jin yadda za ta kaya, shin zai sake zunguro su ko kuwa dai ya kyalesu haka.

“Baba da baka nan, sun zagi ubana”

Shi ne baitin da ya fadi a cikin sabuwar wakarsa wacce yanzu haka za mu sakar mudu odiyonta domin ku saukeshi shi daga shafin nan namu mai albarka.

Ku Saurari Wakar

Madadin mu cika ku da dogon surutu, me zai hana yanzu ku sauke cikakkiyar wakar nan?

To sai gareku.

LATSA NAN DOMIN SAURARON WAKAR

Kammalawa

Ni dai na tabbata mai hali ba ya fasa halinsa, kuma ko ma me zai faru da wuya in Rarara bai sake cin kaniyar mutanenga ba.

Sai dai mu hadu mu ce, Allah ya sawwaka.

Previous News Next News