Sauke Sabuwar Wakar Rarara Mai Taken “Tangal Tangal” Da Kuma Karanta Dalilin Sakinta

Tangal Tangal

Biyo bayan rashin darajar da ‘ya‘yan tafiyar darikar Kwankwasiyya suka yi wa fitaccen mawakin siyasar nanm, Dauda Kahutu Rarara, sakamakon lashe zaben Kano da suka yi ta hanyar kone wa da fashe masa gida da washe komai na cikinsa.

Hadi da washe babban ofishinsa na 13-13 har ma da ofisoshi da ke makwabtaka da nashi, shi ma ya yi waiwaye zuwa garesu.

{tocify} $title={Abubuwan Dake Ciki}

Inda ya saki sabuwar waka wacce a daren jiya (05 ga watan Afrilu) ta hana ‘yan barandan Kwankwasiyya da dama barci inda suka yi ta zage-zage da cin mutunci a kafafen sada zumunta, kai wasu da haufin hakan suka kwana.

Wakar mai taken, “Tangal Tangal” rashin sani yaran tsula ta matukar tayar da hazo hadi da haifar da zazzafar muhawara a dandalin sada zumunta.

Kun ji cikakken labarin muna dauke da shi.

Ku shiya domin jinsa daga A zuwa Z, a karshe kuma mu kawo muku adireshin sauke wakar nan da ya yi kai tsaye.

Su Waye Suka Kone Gidan Mawaki Mawaki Rarara

A safiyar ranar 20 ga watan Maris wadansu fusatattun matasa wadanda ake kyautata zaton ‘yan Kwankwasiyya ne suka fito murnar ‘dan takararsu ya lashe zabe duk da gwamnatin jihar Kano ta sanar da sanya curfew a fadin jihar.

Fitowarsu ke da wuya wasunsu suka yi ta murnarsu cikin salama a kasa da kan ababen hawa, yayin da gungun daruruwan cikinsu suka tafi Zoo Road a fusace da niyyar aikata aika-aika.

Da zuwansu suka yi wa ofishinsa na 13-13 tsinke, suka sace komai na cikinsa kai hatta gilasan tagar ofishin basu bari ba, irin su kujeru, kafet, kayan kida da komai na ciki sai da suka washe.

Kalli hotunan satar:



Ba fa iya nan abin ya tsaya ba, shagunan da suke makwabtaka da nasa ma sai da suka sace komai na cikinsu.

A bangaren guda kuma: karin wasu yaran darikar Kwankwasiyyar sun wuce gidansa na Zoo Road, inda suka fara cinna masa wuta, suka washe komai da komai na gidan.

Kalli hotunan satar:



Tun daga kan baburan da ya ajiye, zuwa kayan abinci, zuwa furnitures, zuwa tagogi da kofofi komai sai da suka sace basu bar masa komai ba.

Shin Jami’an 'Yan Sanda Yi Wani Abu Akai

Kwarai jajirtattun jami’an ‘yan sandan jihar Kano, karkashin jagorancin DSP Kiyawa sun taka muhimmiyar rawa inda suka rinka bin wadannan bata garin magoya baya tafiyar Kwankwasiyya suna ram da su.

Za Ku So: Sabuwar Wakar Rarara Mai Taken "Fadan Karshe" - Ku Sauketa

Sun yi nasarar kama mutane da dama hannu dumu-dumu dauke da kayan da suka sato daga cikin gidan mawakin.

Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda aka damke:




Kuma kamar yadda shugaban ‘yan sandan jihar ya bayyana, za su gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo domin su girbi abinda suka shuka.

Asarar Miliyan Nawa Mawaki Rarara Yayi

Kwana biyu da aukuwar lamarin, wato ranar 22 ga watan Maris, fitaccen mawakin ya fito ya bayyanawa duniya irin asarar da ya yi sakamakon ta’annatin da ‘yan darikar Kwankwasiyya suka yi masa.

Inda ya bayyana wa manema labarai cewa, ya tafka asara da ta kai ta zunzurutun kudi wuri-na-gugar-wuri har Naira Miliyan 800.

Ya kuma kara da cewa, “Ba zan daina fadar sunan Tsula ba saboda tsoron wani ko wata duk da cewa yanzu haka a kiyashin da na yi yaransa sun kwashe tare da kona min kayan gida sama da na miliyan 800, iya na gida kenan ban gama lissafa asarar da na yi a ofishin 13-13 ba idan na gama zan sanar.

In ko haka ne, in muka yi duban tsanaki wa wannan furuci na mawakin nan, za mu ga cewa lallai ya tafka babbar asarar da sai dai muce Allah shi mayar masa da mafificin alkhairi.

Sakin Sabuwar Wakar Tangal Tangal

A daren jiya, mawakin ya saki sabuwar wakarsa mai taken, “Tangal Tangal” inda ya soki yaran darikar Kwankwasiyya ya kirasu da “Tangal Tangal rashin sani yaran tsula.

Ya kuma yi habaice-habaice masu tarin yawa a cikin wakar, wanda hakan sam bai yi wa magoya bayan shugaban darikar Kwankwasiyya dadi ba.

Wannan dalili yasa jiya suka yi ta cin zarafin mahaifiyarsa a soshiyal mediya, inda suke ikirarin wai, “Uwa bata fi Uba ba.”

To, idan muka yi duba na hankali, duba na tsanaki, za mu ga ashe wannan ihunka banzan da yaran darikar Kwankwasiyyar ke yi baki daya borin kunya ne.

Kuma fito da rashin tarbiyya ne karara, domin duk lalacewar uwa, uwa ce. Kuma Rabi’u Musa Kwankwaso ba annabin karshen zamani bane da za a yi masa habaici a siyasa su kuma su tsomo uwar wanda ya yi habaicin.

Ko-da-ya-ke wanzami daman ance baya son jarfa, amma duk wanda ya bibiyi wakokin Rarara tun daga kan na shekarar 2011 irin su “Tabare” zai san cewa kwarai Kwankwasawa ba za su iya lasar kaso 30 din cin mutuncin da suka daure wa mawakansu gindi suka yi a baya ba.

Domin ga shi an yi walkiya kowa ya gansu.

Sannan babu wanda ya cancanci ya kare martabar mahaifinsa face dan da wannan uban ya haifa.

To, tambayar anan ita ce, ina ‘ya‘yan shugaban darikar Kwankwasiyya na cikinsa? Ko dai kurame ne?

Ko dai basu kishin mahaifin nasu?

In ko haka ne, ban ga dalilin da zai sa ‘yan zawiyar darikar Kwankwasiyya su fito suna cin mutuncin wanda ya yi wannan waka ba, domin waka ce ta siyasa, ita ko siyasa yinta ake ba da gaba ba.

Me Ya Kamata ‘Yan Kwankwasiyya Su Yi

Tabbas da ni mai fada aji ne a tafiyar darikar nan, da na sanya mawakanmu su ma sun shiga studio sun yi wa wannan mawaki martani.

Domin shi mawaki, mawaka ne daidai da shi ba sauran mutane irinmu ba, mawakan ne za su yi masa yaren da zai fahimta.

Ina su Tijjani Gandu suke, meye amfaninsu in dai za a ci wa madugun darikar Kwankwasiyya mutunci amma ba za su yi komai ba?

Lallai ya kamata mawakan tafiyar darikar nan su gwangwaje shi, amma ba sauran magoya baya ba.

Ku Sauke Wakar Tangan Tangal

Domin jin duk abinda mawakin nan ya fadi a cikin sabuwar wakar nan tasa da kanku, zan so ku sauke tare da sauraron wakar nan tasa mai taken, “Tangal Tangal” daga shafin nan namu.

LATSAN NAN KU SAUKETA

Bayan kun sauke, sai ku saurareta sannan ku yi alkalanci, shin ku ya kamata ku mai da martanin ihunka banza, ko kuwa mawakan Kwankwasiyya wadanda za su yi amfani da baki (abin magana) su rama muku?

Amsa na gareku, na barku iya haka.

Kammalawa

Da wannan na zo karshen rubutun nan nawa, kuma ina fatan baki daya rubutun nan bai bata wa ko da daya daga cikinku rai ba.

Ita siyasa in za ku yi ta, sai ku rinka yinta ba da gaba ba. Ni dan dai dan Gandujiyya ne kuma dan Kwankwasiyya domin ina son kowanne daga cikinsu hakan yasa na zama neutral.

Za ku iya kalubalantar baki daya rubutun nan, ta hanyar fadar ra’ayinku a karkashin article din nan.

Allah ya kara wa Annabi Daraja.

Previous News Next News