Sabuwar Wakar Dauda Kahutu Rarara Mai Taken Fadan Karshe - Ku Sauketa

Fadan Karshe

Ga fa dukkanin alamu fadan karshen nan dai ya zo, kuma gobe za a yi shi in Allah ya kaimu da ranmu da lafiya.

Gobe ne ranar da dukkanin talakawan Najeriya, da masu dan kudi, da masu kudi, da masu dukiya za su fita kwansu da kwarkwatarsu domin rarrabe tsakanin aya da tsakuwa.

Gobe ce ranar da kiyamar da dama daga cikin ‘yan takarkarun nan na jam’iyyun kasar nan za ta tsaya.

Wadanda za su shiga gidan salama su shiga, na gidan kedco ma za su san matsayinsu.

To

Sai dai fasihin mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara ya ce ba za mu yi zaben nan haka ba ba tare da wata sabuwar waka wacce za ta debe mana kewa ba.

Ku Duba: Sabuwar Wakar Rarara Mai Taken Jagaba Ya Karbi Kasa

Dalilin haka yau, ranar 3 ga watan Mayu ya saki sabuwar waka mai taken, “Fadan Karshe” za ku iya sauketa kai tsaye daga shafin nan namu mai albarka.

Fadan Karshe

Duk inda ka ji ance fadan karshe to ana nufin an gama yin gumurzu, an kuma gama gwagwarmaya, wadanda za su mutu sun mutu, wadanda za su sha suna kan sha.

Za a kashe Boss.

Wato fada ya dawo tsakanin gidan aktawa da kuma basawa.

Ni dai na san a wannan fadan babu wasu aktawa sama da talakawan jihar Kano da ma Najeriya baki daya.

Su kuwa basawa kowa ya riga da ya san su; su ne ‘yan takarkaru. Kuma ina da yakinin gobe ne za su gane kurensu.

Wakar Fadan Karshe

Wohoho! 

Ko kun san kuwa a cikin wakar nan Dauda Kahutu Rarara ya yi ruwan habaici kuwa?

Aradu ya yi su, a ciki kuma cicci mutuncin tsula da kuma yaransa, har ya ke ce musu; “Mu adda Kano ga can Villa”.

Kuma wanda ya dauki nauyin wakar Nafi’u Nafi’u newanda aka fi sani da Junior.

Ban son na cika ku da shegen surutu, za ku iya sauke wakar nan yanzu haka kai tsaye.

LATSA NAN KA SAUKETA

Kammalawa

A nan na ke son yin amfani da wannan dama wurin aje alkalamina, ina kuma rokon Allah (S.W.T.) da ya zaba wa Kanawa shugaba na gari wanda zai zame musu alkhairi.

Previous News Next News