Ku Sauke Sabuwar Wakar Sani Liya Liya Mai Suna Mahaukaciya


A cikin watannin da suka gabata back-to-back fitacce kuma shahararren mawakin nanayen nan, Sani Liya Liya, ya rinka fitar da sabbin wakokin siyasa wadanda ya yi su ga ‘dan takarar da yanzu haka ya sha kaye wato Alhaji Atiku Abubakar.

To, bayan yin duban tsanaki da mawakin ya yi ya ga kuma tafiyarsu fa ta yi burmawar rumbu hakan ya sa ya yi wawan tsalle domin koma wa inda ya fi wayo wato wakokin nishadi.

Yau cikin hikima da yarda ta Allah ga shi mun kawo muku sabuwar wakar Sani Liya Liya mai taken, “Mahaukaciya” za ku iya sauketa kai tsaye ta shafin nan mai albarka.

Kafin nan bari mu dan tsakura muku tarihin mawakin nan ko babu yawa.

Waye Sani Liya Liya

Sani Abdullahi Alhassan wanda aka fi sani da Sani Liya Liya dai mawakin Hausa ne, kuma kamar yadda ya bayyana ya a cikin wani faifan bidiyo ya ce ya fara waka tun wajen shekaru 10 da suka wuce.

Ita ko daukaka sai cikin shekaru biyun nan ya yi ta.

Kuma dalilin daukakarsa ba komai ba ne face wata wakarsa mai taken, “Sambisa” wacce Yamu Baba da Zainab Sambisa suka hau.

A Wanne Gari Yake

Eh to yanzu haka in muka fadi wani abu game da mahaifa ko kuma garin da Sani Liya Liya ya ke to magana ta fisabilillahi kuma ta domin Allah mun yi muku karya.

Iyakaci dai abinda muka sani shi ne, Sani dan Arewacin Najeriya ne domin ko bincike da bidiyen da muka yi a intanit bai bamu da gamsasshen bayani ba game da mawakin.

To, a zargin da muka yi shi ne; gaskiya shi din ba tafiya ya ke da zamani ba. Wannan yasa babu wata kafa da ta wallafa bayanai a kansa.

Wakokinsa

Daga cikin wakokin Sani Liya Liya akwai irin su;

  1. Layi Roka
  2. Atiku Kawai
  3. Sambisa
  4. Atiku Dodo
  5. Yar Larabawa
  6. Anan Na Yada Kudina
  7. Mahaukaciya
  8. Daga Sama Har Kasa
  9. Chanji Kawai
  10. Baban Bola

Wadannan su ne kadan kenan daga cikin wakokinsa. Kuma za ku iya kallo ko sauraronsa a tashar Youtube domin nan ne matattararsu.

Wakar Mahaukaciya

Sai fa kun yi hakuri sakamakon ku da kuka zo sauke wakar Mahaukaciya kun ga mun dauki wata turbar da ku.

Yanzu za ku iya sauke wakarsa sabuwa daga shafin nan mai albarka kai tsaye ba tare da bata lokaci ba.

LATSA NAN KA SAUKETA

Kalli Bidiyon Wakar

Biyion wakar Mahaukaciya dai kamar yadda aka saba Yamu Baba ne angwon Zainab Sambisa suka hau kan wakar.

Za ku iya kallace wakar yanzu a tashar nan ta Youtube.

Kammalawa

Alhamdulillah, yanzu kam komai ya yi ready ya zama daidai. Muna muku matukar godiya bisa ziyartar shafin nan namu mai albarka da kuka yi.

Allah ya kara wa Annabi Daraja.

Previous News Next News