Sirrikan Maza da Mata Ba Su Sansu Ba a Lokacin Jima’i da Kwanciyar Aure.

Akwai wasu mahimman abubuwan da duk namiji yana son ganin matarsa ta masa su a lokacin da zasu gudanar da ko kuma suke yin jima'i ko kuma bayan sun gama.

Sai dai maza da dama basa iya fitowa fili domin su sanar wa matansu irin wadannan abubuwan duk da tsananin son da suke wa su wadannan abubuwan.

A wannan darasin zamu bayyyanawa mata wasu abubuwan da mazajensu suke son ganinsu sun yi musu a awannin gudanar da Jima'i. 

Kamshi da Sanya Turare

Duk namiji yanason jin kamshi a jikin matarsa a lokacin Jima'i.

Bama a jikinta kadai ba hatta a yawun bakinta yana son yaji ta sha wata alawa ko cingam da zai sa bakinta kamshi kamin lokacin Jima'i.

Don haka mata kuyi kokarin ganin bayan anyi wanka a ta batar an fesa turare mai kamshi tare da samun wani alawa, ko cingam da zai sãka bakinki yayi kamshi. 

Wannan babban sirri ne na maza wasu matan basu sani ba suke kwanciyar da mazajensu jikin na tsami baki na yami.

Shigar Kayan Motsa Sha'awa

Wasu matan sai su dauko zane su daura ko wasu kayan da zai rage wa namiji kallon suranta.

Maza suna son ganin matansu sun masu shigan batsa, irin kamfen nan mai kama da bente duwawu a waje rabin nonuwa a wajen da ake kiransu lingerie.

Haka shiga na kayan da suke da sharashara suma maza na bukatar ganin matansu dasu a lokacin Jima'i.

Sadaukar Masa Da Kanki

 A awanni na jima'i maigida yana son ganin matarsa ta mika masa wuya sai yadda yayi da ita sai kuma abunda yace mata tayi.

Wasu matan sukan yi gigiwan nunawa namiji sune zasu jagoranci harkar kwanciyar. Maza basa son hakan. Yafi son ki bi umurnin da zai baki tare kuma da nuna masa abunda kike so da yadda kike so.

Tabbatar masa kina karkashin umurninsa a wannan lokacin. Furta masa kalmar sai abunsonka shine umurninka akaina.

Maza suna matukar son haka a lokacin Jima'i da matansu.

Kalamanki

Maza suna son jin matansu suna musu kalamai na musamman a lokacin harama da saduwa. A wannan yanayin namiji yana son wasu kalaman da zasu sake kara masa kuzari da marmari.

Kalamai na batsa irin "daren yau ina son na jika har wuya". Ko kuma "ina son ci na musamman a yau". Ireiren wadannan kalamai maza na matukar son jinsu daga bakunan matansu a lokacin shirin saduwa dasu.

Kukan Kissa

Shi kukan Kissa shike aikawa namijin sakon halin da matarsa take ciki a lokacin da yake Jima'i da ita.

Duk matar da tayi gum ana saduwa da ita tamkar mijinta na mata fyade wannan macen bata jiyar da mijinta wani dadi koda kuwa yana jin dadin.

Shi kuka kissa a wajen mace dan sako ne da zata rika ambato yadda take ji da kuma furtawa mijinta ya yi mata yadda take so tare kuma da kambamashj na irin dadin da yake jiyar da ita.

Don haka kukan kissa a wajen maza a yayin Jima'i wani sinadari dake sa Jima'i armashi da idan babu shi babu dadin Jima'i.

Saki jikinki da muryarki yi kukan ki da rakinki yadda kike so ba tare da kinji shakku ko kunyar kowa ba. Shi yasa wasu magidanta idan mace mai raki garesu na kukan dadi suke kunna kida musamman idan suna tunanin akwai masu iya jiyo muryar ta.

Sadarwa

Akasarin maza ba fahimtar abunda mace keso suke yi ba cikin sauki. Don haka maza kan bukaci mace a lokacin saduwa tana fadawa mijinta yadda take so yayi mata ko ya taba mata.

Idan kina so ya bidake a hankali ne kece zaki sanar masa. Haka nan idan kina bukatar ya bugaki da karfi kuma da sauri.

Idan kina son yana sha bakinki ko nonuwanki a lokacin da yake cikinki duk wannan sai kin fadamasa sannan zai yi.

Kada ki bari namiji yana miki abunda kika san baki so ko bai gamsar dake a lokacin Jima'i da mijinki. Yi amfani da sadarwan Jima'i domin sanar dashi abunda kike so ko kika fi so.

Duk wannan na daga cikin karatuttukan tsangayar malam tonga. Allah ya kara wa malam lafiya da nisan kwana.

Previous News Next News