Abubuwan 11 Da Ke Karawa Maza Karfin Azzakari da Kuzari Yayin Jima’i

Karfin Azzakari

Mafi akasarin mazaje musamman Hausawa suna Allah wadai da motsa jiki daga lokacin da suka tsallake ganiyar samartaka, ga kuma jarabar shan maganin kara karfin kutuma saboda son cin duri.

Sai su kekashe su yi kememe wurin kin motsa jiki, gasu da masifaffiyar son duri da ragargazarsa.

In har gaske ka kasance masoyin cin duri akai-akai, to wannan rubutun namu na yau na ke ne.

Domin kuwa yau za mu kawo muku wadansu kayayyakin ci da sha har ma da yi wadanda ke karawa maza karfin azzakari da kuzari yayin soke kunkurun matsin cinya cikin dare ko da ranar Allah.

Kada ku ce na baci da yawa, karatun namu ne yau ya zo da haka, kuma dolen-dole mu fadi mu kara fadakar da mutane.

Kada na addabeku da dan banzan surutu, ga su nan kamar haka.

1. Danyen Madara

Ku rinka yawan shan danyen madara musamman na shanu wanda aka bankwar ba hakan na kara karfin azzakari da kuzari ga da namiji.

Amma ba laifi ba ne, in har ka samu nono kindirmo ka sha, ko kuma ka laludi yoghurt ka sha kuma ka ke sha a kan kari.

Ku yawaita sha madara ko da ta kirjin matanku ce. Allah ya baku diya na gari. Ameen.

2. Zuma

Kowa ya sani duri ya fi zuma dadi duk da cewa zuma ya fi shi zaki. Amma in dai kana son karin kuzari wurin tumurmusar duri to a shawarce ka yawaita shan zuma.

In ba ka da hanyar samunta kusakusa, to ka je Kano kasuwar kurmi za ka samu zuma irin wacce ka ke so.

Yawaita shan zuma na da nasa alfanun ga karin kuzari yayin jima’i.

3. Motsa Jiki

Motsa Jiki wanda a turance ake cewa, gyming ko workout hanya ce mafi sauki da tasiri wurin karawa jiki lafiya da kuma kara wa jiki kuzari da dogon zango yayin jima’i.

Mutumin da ya ke yawan motsa jiki akai-akai to tabbas ko bai nemi maganin kara karfin maza ba, zai iya gurzar matarsa ya more, kuma zai iya gamsar da ita muddin ya san ta kan abun.

Saboda haka a shawarce mutanenmu maza da mata Hausawa kuma ‘yan Arewa ku rinka motsa jiki akai-akai, ba wai sai dole ka samu rashin lafiya likita ya ce ka rinka motsa jiki sannan za ka fara ba.

4. Danyen Rogo

Dukkanin mutanen birane, karkara da kauyuka sun san menene dafaffen rogo wanda ake yinsa a garkar rogo.

Amma samun danyen rogo shi ne aiki ga mutumin da ba a kauye yake ba, mutanen birni ana kai musu dafaffe, amma ba a cika kai musu danye ba sai busasshen alabo ko kuma dafaffen rogo.

In dai ka san inda za ka samu danyen rogo wanda ake ci ba wanda ake alabo da shi ba, to ka samu ka rinka garzarsa lokaci zuwa lokaci zai kara wa azzakarinka karfi da lafiya.

5. Dabino

Amfanin dabino ga lafiyar dan adam da shi kansa dan adam ba za su lissaftu ba, hakan ya sa shi kansa mazo ya umarcemu da cin dabino lokaci zuwa lokaci.

In dai kana son azzakarinka ya kara lafiya da lasting yayin soke kunkuru, to ka rinka yawan cin dabino akai-akai.

In dai ka dage da yin hakan hadi da motsa jiki ga cin kayan marmari to lallai za ka zama gwarzon sadauki kuma sarkin yaki a shimfidar bacci.

Matarka za ta yaba da kwazonka wajen cin duri da yin dogon zango yayin cin durin kwarai da gaske.

5. Kwakwa

An zo wajen, an kuma karaso wurin.

Yana da matukar amfani da fa’ida a garemu mu dage wajen cin kwakwa in dai muna son azzakarinmu ya kara karfi kuma mu samu kuzari yayin yakin raba raini tsakaninmu da duri da daddare.

Kuma kwakwa na da dadin ci kwarai da gaske yayin da aka hadata da dabino wuri guda. Shi yasa da wuya ka tarar da mai siyar da kwakwa ba ya siyar da dabino.

Ka yawaita cin kwakwa da dabino in dai kana son ka samun karin kuzari yayin jima’i, da karfin azzakari.

7. Kayan Marmari

Kayan marmari na da matukar amfani ga lafiyar ‘yan adam, saboda haka ku yawaita shan kayan marmari domin samun karin karfin azzakari da kuzari yayin soke kunkuru.

Ba kuma iya maza ba, mata ma su yawaita shan kayan marmari domin zai kara musu ruwa irin na ni’ima da kuma dadi yayin da ake saduwa da su.

A shawarce a rinka cinsu yadda ya kamata.

8. Waken Suya

Waken suya da nau’ikan abincin da aka yi da shi, ku rinka cinsu domin suna kara lafiyar zakari.

Ni dai abin da na sani wanda ya shahara ake yinda da waken suya awara ce. Ko-da-ya-ke zamani ya canza yanzu ana yin abubuwa masu tarin yawa na ci da waken suya.

Amma ku rinka cin abincin da aka yi da waken suya domin samun karin lafiyar gaba da kuma kuzari yayin jima’i.

Sai dai duk da haka kada ku manta da motsa jiki, domin shi ne a kan gaba wurin kara lafiyar gaba daya jikin dan adam ba wai iya gabansa ba.

Allah ya kyauta.

9. Ginger / Citta

Ginger na nufin citta, ni dai a nawa bangaren ba na son citta bare cinta, amma dai na san ana hadata da abubuwa masu tarin yawa wurin yin abinci da sauransu.

Ku rinka cin citta domin samun karin kuzari da kuma karfin gaba, amma fa in kun ga za ku iya.

Duk wanda ya san ba zai iya cin citta ba, ya shafa wa kansa ruwan sanyi, ya kuma yi wa kansa kiyamullaili ya nemi alternative solutions kamar su motsa jiki, shan kayan marmari da sauransu.

10. Abinci Mai Nauyi

A likitance ban sani ba ko abinci mai nauyi na kara karfin gaba da kuzari yayin jimai.

Amma dai abinda na sani shi ne; duk wanda zai samu abinci mai rai da lafiya ya dirka to zai ji garau a jikinsa, in ko ya ji garau to zai iya ragargazar matarsa yadda ya ke so.

Sai dai abinci mai nauyi ba yana nufin tuwo irin na dawa da miyar da babu kayan hadi ba, abinci ake nufi na hakika.

11. Namijin Goro

Kusan kowa ya sani, namijin goro na kara kuzari da karfin gaba kafin aci duri. Domin wasu magidantan na tauna shi ne mintuna 30 kafin su je ga matansu.

Kai ma za ka iya samun namijin goro ka ci mintuna 30 kafin ka je ga iyalinka, na tabbata zai taimaka wurin tada jijiyoyin gabanka ya kara ma kuzarin yayin jima’i.

A Karshe

Kai ne da mata, kai ka san rauninka. Saboda haka ku tashi tsaye ku yawaita motsa jiki da yawan cin abinci mai gina jiki.

Ni a ganina, yawan neman maganin karfin maza na ga magidantan da basa son motsa jiki kuma gasu da son cin gindi. Saboda haka don Allah ku dage wurin motsa jiki duk da tension da stress din da ake fama da shi a kasarmu ta gado wato Najeriya.

A karshe, ina mai addu’ar Allah ya shiryar da mu ya kuma kara wa Annabi Muhammadu Mai Tsira da Amincin Allah Daraja.

Previous News Next News