Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya zama sabon shugaban ECOWAS

Bola Ahmed Tinubu


Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS).

Tinubu ya zama shugaban kungiyar ne a taro na 63 na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS da aka yi a Bissau, babban birnin Jamhuriyar Guinea-Bissau.

Da yake jawabi bayan mika mulki daga hannun tsohon shugaban kungiyar na yankin, Shugaba Tinubu ya ce: "Za mu dauki dimokuradiyya da muhimmanci, dimokuradiyya tana da matukar wahala amma ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati."

Tun da farko, kasashe mambobin kungiyar ECOWAS sun nuna godiya da taya murna kan yadda zaben Najeriya ya yi nasara wanda ya kai ga samun nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Tsohon shugaban kungiyar na yankin kuma shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló a jawabinsa na bude taron ya yabawa Najeriya kan samar da zaman lafiya da karfafa dimokuradiyya a yankin yammacin Afirka.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray, a madadin al’umma da cibiyoyi ya taya Shugaba Tinubu murnar zaɓen sa da kuma hawansa kujerarsa a matsayin Shugaban Nijeriya wanda ita ce mafi girmar tattalin arziki da ƙasa a Afirka.

Touray ya bayyana godiya ga shugaba Embaló bisa jagorancin da ya yi a matsayinsa na shugaban ECOWAS a cikin watanni goma sha biyu da suka gabata inda ya bayyana cewa al’ummar yankin sun samu nasarori da dama.

Ya kuma taya shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio murnar sake zabensa.

Previous News Next News