Akan cacar baki, amarya ta kashe mijinta ta hanyar caka masa wuka a kirji a jihar Bauchi

Wata sabuwar amarya ‘yar shekara 21 ta kashe mijinta har lahira ta hanyar caka masa wuka a kirji cikin dare a jihar Bauchi.

Amaryar mai suna Maimunatu Sulaiman ta kashe mijinta mai suna Aliyu Muhammad shekaranjiya da daddare.

Kamar yadda ta bayyana wa 'yan sanda masu bincike, ta ce cacar baki ce ta shiga tsakaninta da mijinta, sai da ta bari sun kwanta a kan gadonsu da nufin za su yi bacci bayan kammala cacar bakin, sai ta dauko wuka ta caka masa a kirjinsa wanda hakan yayi ajalinsa

Kamar yadda jami’in ‘dan sanda, Datti Assalafiy ya wallafa, ya ce yanzu haka tana nan a shashin binciken manyan laifuka na ‘yan sandan jihar Bachi, kuma in an kammala bincike za a gurfanar da ita a gaban kuliya.

Kalli cikakken labarin cikin hotuna;

Maimunatu Sulaiman

Aliyu Muhammad's corpse

Aliyu Muhammad's death bed

Bride Maimunatu and the late groom Aliyu


Previous News Next News