Maganin Sanyi Infection na Mata (Alamominsa da Abinda ke Kawo Shi)

Sanyi Infection
Sanyi Infection

Ya zama wajibi mu tausaya wa mata wadanda suke da cutar ciwon sanyi (infection) domin ko ba komai suna cikin matsala.

La shakka, mata iyayenmu ne, don haka dole matsalar da ta same su, mu ma ta same mu.

Shi kuma ciwon sanyi ba ga iya mata kadai ya tsaya ba, a’a, har mazan ma suna fama da shi.

Sai dai na maza da na mata mafi akasarin lokuta ya kan bambanta.

Sanyi infection na mata ciwo ne da ke sanya mace ta rinka kurajen gaba, ta na jin gabanta na kaikayi, ko gabanta ya na fidda farin ruwa mai wari, ko kuma ta na fama da matsalar rashin sha’awa ko rashin gamsuwa yayin da ake saduwa da ita da sauransu.

Ciwon sanyi na maza shi kuma mafi akasarin lokuta ya kan sa namiji kurajen kan azzakari, kankancewar gaba, daukewar sha’awa, fitar farin ruwa daga kwarkwaron azzakari da sauransu.

Yadda maza ke daukar nasu sanyin ya ‘dan sha bamban da yadda mata ke dauka.

Domin da wuya namiji saboda yana fitsari a bandaki maras tsafta infection ya kama shi, amma ita mace in tana yi, to, babu tantama infection zai iya kama ta.

Recommended Reading: Maganin Sanyi Kowanne Iri

Kamar yadda sha’awa kan daukewa maza dalilin sanyi, to su ma matan haka ne.

Haka kuma, kaikayin gaba da kurajen gaba wannan sanyi bai dauke wa maza ba bare mata.

Alamomin Ciwon Sanyi (Infection)

Kowacce irin cuta na da nata alamomin da ta ke nunawa. Saboda haka shi ma sanyi ba zai barranta ba.

Daga cikin alamominsa akwai;

  • Yana sa ciwon mara (mai tsanani)
  • Da daukewar sha’awa 
  • Kurajen gaba
  • Fitar jinin al’ada baki kirin da wari
  • Fitar farin ruwa mai wari daga farjin mace
  • Mace ta rinka jin zafi yayin da ake saduwa da ita
  • In ko ya yi karfi, yana iya hana mace haihuwa dss.

Hakikanin gaskiya alamomi sanyi (infection) na mata suna da yawa, amma dai za mu takaita a kan iya bakwai din da ke sama.

Me ke Kawo Ciwon Sanyi (Infection)

Abubuwa da dama ka iya haifar da kamuwa da ciwon sanyi ga mata, daga cikinsu akwai;

  • Yawan tsarki da ruwan da zafinsa ya yi yawa
  • Yawan yin tsarki da ruwan sanyi
  • Cin danyar albasa
  • Saduwa da mai cutar
  • Fitsari a bandaki maras tsafta da sauransu.

Sai dai tsafta na taimakawa sosai wurin rage yaduwar cututtuka, sannan yi wa jiki da ciki sabis shi ma kan taimakawa wurin rage harbuwa da cututtuka.

Maganin Sanyi Infection

Akwai nau’ikan magungunan sanyi (infection) na mata masu tarin yawa, za mu fara kawo muku su daki-daki, hadi da yadda ake hada su.

Shi wannan da za mu bada yanzu, yana maganin dattin mara, yana kuma maganin fitar ruwa (sanyi) daga gaba.

Domin hada shi.

Ku nemi;

  1. Garafuni
  2. Sassaken sanya

Yadda Ake Hada Shi

Kuna samun sassaken sanyarku da garafuninku, sai ku saka su a tukunya, ku kawo ruwa ku kela a kansu.

Daga nan sai ku hada wuta, ku dora tukunyar a kai ku cigaba da izawa har sai ya tafasa.

Sai ku sauke, bayan kun sauke sai ku barshi ya huce, daga nan sai a rinka diban rabin kofi da safe, rabin kofi da yamma ana sha.

Insha Allahu za a samu sauki daga lalurar sanyin da ta ke damunku.

Maganin Sanyi (Hadi na Biyu)

Wannan ga wasu zai iya yin wahala, amma ga masu zaman karkara ba zai wahala ba.

Ku samu furen tumfafiya sai ku shanya shi ya bushe.

Bayan ya bushe, sai ku daka shi ya yi lukwui, sannan sai ku na siyan nono (kindirmo) kuna diban garin furen tumfafiyar nan kuna zubawa a ciki kuna sha.

Da yardar Allah za ku samu rangwame daga lalurar sanyi infection.

Maganin Ciwon Sanyi Infection (Hadi na Uku)

Shi ko wannan hadin da zogale ake hada shi, kuma yana aiki kwarai da gaske.

Ku samu ganyen zogale, sai ku dafa shi.

Bayan ya dahu sai ku murjeshi ku tace ku yi lemon juice da shi, sai ku samu madara ko nono ku zuba, ku kawo zuma ku zuba.

Sai a sha.

Ku cigaba da yin haka na ‘dan lokaci mai tsayi, Insha Allahu sauki zai samu.

Kammalawa

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) da ya bani damar kammala wannan jawabi nawa.

A cikin rubutun nan na yi bayani a kan menen ciwon sanyi, alamomin ciwon sanyi, me ke kawo shi da kuma maganinsa.

Ku yi sharhi.

Previous News Next News