Hamisu Breaker - Ba Yanzu Ba LyricsBa yanzu ba

(Sultan with the beat baby)

Ba yanzu ba

Sai dare, sai dare ya tsala

Ba yanzu ba

A jira, a jira, a jira, a jira sai gobe

Ba yanzu ba

Rabuwar mu da ita sai goben da bata da gobe

Ba yanzu ba

Hakurin ta dani shike sani in ce gobe

Ba yanzu ba

Sai kaji nace gobe

Ba yanzu ba

Wallah ni bana so

Ba yanzu ba

Yanda nake kaunar ta a zuci zan baku labari

Ba yanzu ba

A barshi na fasa ma

Ba yanzu ba

Sai bayan kun girma

Ba yanzu ba

Kun bar nema na ma

Ba yanzu ba

Sai dai neman nema

Ba yanzu ba

Sai in tuna maku

Ba yanzu ba

Duk maganar da muke yanzu-yanzu kuma dai anjima ma ba

Ba yanzu ba

Ko zaku gane nufi na?

Ba yanzu ba

Nasan bakwa gane ba

Ba yanzu ba

Bari in jingine maganar nan

Ba yanzu ba

Sai anjima shikenan

Ba yanzu ba

Sai girma ya karu

Ba yanzu ba

Shekaru sun taru

Ba yanzu ba

Ni bana son daru

Ba yanzu ba

A yanzu ban son daru

Ba yanzu ba

Bana kaunar daru

Ba yanzu ba

Masu tsokano rigimar nan

Ba yanzu ba

Ku bari a jima mana

Ba yanzu ba

Haba ku barmu don Allah mana

Ba yanzu ba

Ko so zai magana?

Ba yanzu ba

Ba zaya canza halayya ba

Ba yanzu ba

Kuma koda zamu tuna

Ba yanzu ba

Ba zamu daina duka mai ba

Ba yanzu ba

Ku jira kanin ajali

Ba yanzu ba

Da yazo da kansa kani

Ba yanzu ba

Ku barshi don Allah mana

Ba yanzu ba

Ku bar mu don Allah

Ba yanzu ba

Sai dare, sai dare ya tsala

Ba yanzu ba

A jira, a jira, a jira, a jira sai gobe

Ba yanzu ba

Rabuwar mu da ita sai goben da bata da gobe

Ba yanzu ba

Sai kaji nace gobe

Ba yanzu ba

Wallah ni bana so

Ba yanzu ba

Masoyiya ta, masoyiya ta tun

Ba yanzu ba

Tana yabawa da kaunar da nayi mata tun

Ba yanzu ba

Masoyiya ta, masoyiya ta tun

Ba yanzu ba

Tana yabawa da kaunar da nayi mata tun

Ba yanzu ba

Sai dare, sai dare ya tsala

Ba yanzu ba

Ku jira, a jira, a jira, a jira sai gobe

Ba yanzu ba

Ni ina gode maki tun-tun

Ba yanzu ba

Kana ina ta yaba miki tun-tun

Ba yanzu ba

Dole in nuna miki so ko

Ba yanzu ba

Kuma za'a yaba mana ni dake ko

Ba yanzu ba

Ku dakata makiyan mu

Ba yanzu ba

Mai son ganin bayan mu

Ba yanzu ba

Mai ce kawai ku jira mu

Ba yanzu ba

Kai mai son ka raba mu

Ba yanzu ba

To fah baza ka iya ba

Ba yanzu ba

Kema ba zaki iya ba

Ba yanzu ba

Wanda yace mu tsaya

Ba yanzu ba

To fah ba zamu tsaya ba

Ba yanzu ba

Mai burin karaya

Ba yanzu ba

To fah bazan karayan ba

Ba yanzu ba

Mai son yimin wayo

Ba yanzu ba

Naki wayon tun

Ba yanzu ba

Muna ta so ne tun

Ba yanzu ba

Muna ta kauna tun

Ba yanzu ba

Muna ta raino tun

Ba yanzu ba

Mun gina tuni tun

Ba yanzu ba

Sai dare, sai dare ya tsala

Ba yanzu ba

A jira, a jira, a jira, a jira sai gobe

Ba yanzu ba

Rabuwar mu da ita sai goben da bata da gobe

Ba yanzu ba

Sai kaji nace gobe

Ba yanzu ba

Wallah ni bana so


Written by Hamisu Breaker

Previous News Next News